Coronavirus: Hannayen Jarin Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Faduwa

Hannayen jarin Kasuwanni duniya na ci gaba da faduwa a yau Juma’a sakamakon fargaba dake kara yaduwa cikin sauri fiye da cutar coronavirus.

Cutar da ake yiwa suna COVID-19 ta haifar da matsala wurin shigar da kaya, sabili da haramta tafiye tafiye, lamarin dake kawo cikas ga hada hada da cinikayya a duniya.

Masu fashin baki sun yi hasashen cewa, wannan mako zai fi muni fiye da cikas da harkokin kudi a duniya ya huskanta a shekarar 2008.

Wannan wani lokaci ne maras tabbas, babu wanda ya san hanyar shawo kan wannan matsala kana kasuwanni na cikin tsananin fargaba, inji John Lau, shugaban wata babbar kasuwar yankin Asia ta SEI Investments Head of Asian Equities, yana fadawa manema labarai.

Kasuwar Japan da China ta fadi a ayau Juma’a da kashi 3.7 cikin dari, yayin da Korea ta Kudu da Australia suma suka fado da sama da kashi 3 cikin dari. Kasuwannin turai kuma sun yi kasa da kashi 2.3 cikin dari.