COVID-19: An Zargi Gwamnatin Zimbabwe Da Nuna Bambanci a Bada Tallafi

A Zimbabwe, matakan hana zirga-zirga da hukumomin kasar suka dauka sanadiyyar cutar COVID-19 da suka hada da rufe kasuwanni sun sa jama’ar kasar da dama cikin kangin rashin aikin yi da samun abinci.

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta fitar a wannan makon, ya yi zargin ana hana wasu jama’ar kasar abincin tallafi saboda ba sa goyon bayan jam’iyyar ZANU-PF mai Mulki.

Wani mutum da ke zaune a yankin da ake kira Murehwa da ke da nisan kilomita 100 daga Harare babban birnin kasar, wanda kuma ya nemi a sakaya sunansa da Peter, ya fada wa Muryar Amurka cewa ana mayar da magoya bayan jam’iyyun adawa saniyar ware.

Ya ce, “shugabannin yankin ‘yan jam’iyyar ZANU-PF ne, duk wanda ba dan jam’iyyar ba ne ba a ba shi tallafin abinci, sukan ce mana mu je jam’iyyun da muke mara wa baya su ba mu.”

Sai dai karamin Ministan yada labarai a kasar ta Zimbabwe, Energy Mutodi, ya musanta wannan zargi.

Ya ce, “duk labaran ba su da tushe balle makama, sam ba su yi na’am da su ba, muna raba abincin ne ga kowanne dan kasa da ya cancanci a ba shi,” a cewarsa.