COVID-19: "Gwamnati Ba Za ta Dauki Nauyin Masu Dawowa Gida Ba" - Ferdinand Nwonye

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce, daga yanzu duk ‘yan Najeriya da za su dawo gida daga kasashen waje, su ne zasu dauki nauyin masauki, abinci da walwalar kansu.

Tun ranar 6 ga watannan ne ayarin farko na ‘yan Najeriya su 256 suka dawo gida daga kasar Dubai, inda ayari na biyu su 253 suka dawo daga Birtaniyya a ranar 8 ga wata, daga bisani ayari na uku su 160 suka iso babban birnin Abuja daga kasar Amurka a ranar lahadin da ta gabata.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta killace ayarin ‘yan Najeriya 160 da suka dawo gida daga Amurka a wani Otel a birnin Abuja.

A lokacin da wakilan muryar Amurka suka isa filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe, ma’aikatan filin ba su bari an shiga inda ayarin mutane da suka dawo suke ba, saboda ba'a ma bari sun shigo inda aka saba barin fasinjoji su bi ba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Ferdinand Nwonye, ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ce ta dauki nayin tikitin jirgi na ayarin ‘yan kasar da suka dawo gida, amma daga yanzu duk wani dan Najeriya da zai dawo, to zai dauki nauyin masauki da kula da bukatunsa a duk inda zai sauka.

Mahaifin daya daga cikin ‘yan Najeriya da suka dawo gida wanda ya bukaci a yi magana da shi ba tare da daukar sauti ba ya tabbatar da cewa, shi ya biya kudin tikitin dan sa.

A wani bangare kuma, jagoran kwamitin ko-ta-kwana na gwamnatin tarayya, Dr. Sani Aliyu, ya bayyana cewa, duk wadanda suka dawo gida an killace su ne a dakuna daban-daban na otal-otal domin a tantance ko suna dauke da cutar COVID-19.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya ce, gwamnatin tarayya na aiki tukuru wajen dawo da sauran ‘yan Najeriya da suka makale a wajen gida.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Halima Abdulrauf.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ba Za ta Dauki Nauyin Masu Dawowa Gida Ba: Ferdinand Nwonye