COVID-19: Masu Larurar Makanta Sun Ce Ana Cin Zarafinsu

Wasu masu larurar ido a Maiduguri

Kungiyar masu larurar makanta a arewacin Najeriya ta koka kan zargin cin zarafin da ta ce ana yi wa mambobinta da sunan yaki da yaduwar cutar coronavirus a jihar Nejar Najeria.

Shugabannin kungiyar sun ce ana yi musu kamun kan mai uwa da wabi a garin Suleja ana kuma ajiye su a hannun ‘yan banga a cikin yanayi na rashin kulawa.

Sakataren yada labarai na kungiyar a arewacin Najeriya, Kwamred Muntari Saleh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Muryar Amurka.

A cewarsa, ba a ba mambobinsu abinci Kuma an ajiye su a cikin yanayin na rashin tsafta, duk da cewa gwaji ya nuna cewa ba sa dauke da cutar ta coronavirus.

Sai dai shugaban kwamitin yaki da yaduwar cutar coronavirus a jihar Neja wanda kuma shi ne sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya ce bai da masaniya kan wannan lamari.

Sai dai ya ba da tabbacin cewa zai yi bincike domin gano gaskiyar lamarin.

A ranar Litanin 11 ga watan Mayu ne wa’adin dokar hana fita ta tsawon mako biyu karo na biyu da gwamnatin jihar ta kafa domin hana yaduwar coronavirus ya kare.

Har yanzu dai gwamnatin jihar ba ta dauki wani sabon mataki ba dangane da wannan al’amari.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Masu Larurar Makanta Sun Ce Ana Cin Zarafinsu