COVID-19: ‘Yan Afghanistan Da Yawa Sun Bar Iran Zuwa Kasarsu

Wani rahoton kamfanin dillancin labaran Associate Press (AP) ya bayyana cewa akalla ‘yan kasar Afghanistan mazauna Iran 200,000 suka koma gida a ‘yan makonnin nan sakamakon annobar cutar coronavirus (COVID-19) a Iran.

Rahoton ya ce ‘yan Afghanistan mazauna Iran suna ficewa ne daga kasar da take daya daga cikin kasashen duniya da annobar ta fi kamari, zuwa kasarsu ta asali wadda ita kuma bata yi wani tanadi na shirin yakar cutar ba.

‘Yan Afghanistan suna komawa kasarsu ba tare da an gwada ko suna dauke da cutar ba ko a'a. Kamfanin dillancin labaran na AP ya kuma ce mutanen dake komawa suna iya zama sanadin samun barkewar annobar a kasar, lamarin da zai iya fin karfin asibitocin dake kasar.

Jami’an Afghanistan sun ce suna fargabar Iran zata tilasta fitar da ‘yan Afghanistan kusan miliyan daya daga Iran.

Kungiyar kasa-da-kasa ta ‘yan gudun hijira ta ce fiye da ‘yan Afghanistan 145,000 ne suka koma gida a watan jiya, saboda barkewar annobar coronavirus.

Iran na da mutane sama da 58,000 da suka kamu da cutar coronavirus, a Afghanistan kuma mutun 367 kacal, a cewar tsangayar binciken annobar COVID-19 ta jami’ar Johns Hopkins.