Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kasar Sudan Ya Kashe Mutum Biyu a Faransa


Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Wani dan gudun hijira dan asalin kasar Sudan, ya kashe mutum biyu bayan da ya far wa mutane da wuka a Faransa.

Harin wanda ake mai kallon na ta’addanci ne ya auku ne a kudu maso gabashin kasar a ranar Asabar kamar yadda Kamfanin Dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da harin wanda ya auku da tsakar rana yayin da mafi aksarin mutane ke kulle a gidajensu a wani mataki na dakile yaduwar cutar coronavirus.

Hukumomin sun bayyana sunan mutumin a matsayin Abdallah A.-O wanda shekarunsa suka haura 30.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG