CPC Ta Amince Da Hadaka

  • Ibrahim Garba

Janar Muhammadu Buhari Mai ritaya, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar CPC, jam'iyyar masu neman chanji.

A wani taron da ta yi yau a babban birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, jam'iyyar adawa ta CPC ta amince ta shiga sabuwar jam'iyyar hadaka ta APC.
Jiga-jigan jam'iyyar adawa ta CPC da sauran 'yan jam'iyyar, sun amince da shigar jam'iyyarsu cikin jam'iyyar hadaka ta APC.

A wani taron da ta yi yau a babban birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, jam'iyyar ta amince da shiga hadakar idan an kammala dukkan komai ciki har da amincewar hukumar zabe da kuma rajistar jam'iyyar hadakar ta APC. Wakilinmu a Abuja Nasiru Adamu Elhekaya, ya ruwaito Sakataren Jam'iyyar ta CPC Malam Buba Galadima na cewa CPC za ta cigaba da gudanar da ayyukanta a matsayin CPC har sai lokacin da sabuwar jam'iyyar hadakar ta APC ta sami amincewa hukumar zabe a hukumance da kuma amincewa babban taron CPC da za a yi nan gaba.

Your browser doesn’t support HTML5

CPC Ta Amince Da Hadaka- 2.24'


Tun da farko dai madugun jam'iyyar ta CPC Janar Muhammadu Buhari Mai Ritaya, ya yi takaicin yadda ake samun rashin ingantattun matakan tsaro a arewacin Nijeriya da kuma yadda wasu ke daukar cin zabe ko mulki abin ko ayi ko a mutu.