Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CPC Ta Yi Taranto Na Yankin Arewa Maso Gabas A Bauchi


Janar Muhammadu Buhari, mai ritaya, jigon jam'iyyar CPC a Najeriya

An kaddamar da wakilan da uwar jam'iyyar ta kasa ta kafa domin tsara yadda CPC zata hade da wasu jam'iyyun hamayya su koma APC da nufin kalubalantar PDP mai mulki

A yayin da ake bayyana tababar yiwuwar gudanar da babban taron jam'iyyar CPC gobe asabar, rassan jam'iyyar a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun gudanar da taro a Bauchi, domin tsara yadda wannan jam'iyya zata hade da sauran jam'iyyun adawa wajen kalubalantar jam'iyyar PDP mai mulki a zaben 2015.

Taron ya kaddamar da wakilan jam'iyyar wadanda uwar jam'iyya ta kasa ta nada domin jagorancin tsare-tsaren hadewar, da kuma kimtsa ita kanta jam'iyyar ta CPC domin hadewa da masu adawa su kioma sabuwar jam'iyya ta APC.

Daya daga cikin jigogin jam'iyyar a Jihar Bauchi, Injiniya Sadiq Mahmud, yayi karin bayanin wannan taron nasu ma wakilinmu Abdulwahab Muhammad:

Rahoto Kan Taron jam'iyyar CPC Na Yankin Arewa Maso Gabas A Bauchi - 3:12
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG