Cutar Ebola Ta Sake Kashe Wani A Kasar Congo

Wani Malami na amfani da na’urar auna zafin jiki domin neman alamun cutar Ebola.

Ma’aikatar lafiya ta kasar Congo ta sanar da mutuwar wani kuma yau lahadi wanda ya kamu da cutar Ebola.

An sami Karin wadansu mutane hudu da suke dauke da kwayar cutar ta Ebola a damokaradiyar jamhuriyar Kwango, bisa ga cewar ma’aikatar lafiyar a sanarwar da ta fitar ta baya bayan nan.

Kawo yanzu, an bada rahoton cewa, mutane arba’in da shida suka kamu da zazzabin mai sa zubar jinni tunda aka sami barkewar cutar.

Shugaban kasar Joseph Kabila da majalisarsa sun tsaida shawara jiya asabar su kara yawan kudin da ake kashewa wajen gudanar da agajin gaggawa a kokarin shawo kan cutar Ebola, da zai kai sama da dala miliyan hudu