Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Mutane Uku Da Cutar Ebola a Jamhuriyar Congo


An tabbatar samun wadansu mutane uku dauke da kwayar cutar Ebola a Damokaradiyar Jamhuriyar Congo, bisa ga cewar ministan lafiya na kasar.

Ministan lafiyan Oly Ilunga ya fada jiya juma’a da yamma cewa, an sami wadansu sababbin kamuwa da cutar mai kisa a birnin Mbandaka, mai yawan mutane miliyan daya da dubu dari biyu, inda aka sami wani dauke da cutar kwanaki.

Mutane arba’in da uku sun kamu da zazzabin nan mai zafi dake haifar da zubar jinni a yankin,inda aka tabbatar goma sha bakwai daga cikinsu suna dauke da cutar ta Ebola, ana tsammani ishirin da daya daga cikinsu sun kamu da cutar ne, yayinda kuma ake kyautata zaton mutane biyar sun kamu da cutar, inji Ilungu.

Hukumar lafiya ta duniya taki ayyana barkewar cutar a matsayin wani lamarin dake bukatar agajin kasa da kasa na gaggawa, sai dai tace hadarin yiwuwar bazuwar cutar a kasar yana da girma. Hukumar lafiyar ta kuma bayyana cewa, mai yiwuwa ne kuma cutar ta bazu zuwa kasashe tare dake makwabta, sai dai tace babu bukatar kafa dokar kayyade zirga zirga a yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG