Cutar Kwalara ta Barke a Jihar Bauchi

An samu barkewar cutar amai da gudawa, ko kuma “Cholera” a turance, a Jihar Bauci.

Da yake jawabi, shugaban hukumar inganta lafiya a matakin farko Adamu Ibrahim Gamawa yace “a yanzu haka, an samu bulluwar cutar a nan da can, amma ba abun tashin hankali bane.”

“Ya kara da cewa muhimmin abu shine idan akwai rijiya ruwan da yak e zubowa na sama bai dauki datti ya koma da shi cikin rijiya ba kuma a tabbatar da cewa inda babu ruwan rijiya ko rijiyar burtsatse a dafa ruwan an kuma bar shi ya huce.”

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Kwalara ta Barke a Jihar Bauchi - 3'23"