Cutar Kwalara Ta Barke a Wasu Kananan Hukumomin Jihar Kano

Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

An samu barkewar cutar kwalara a wasu kananan hukumomin jihar Kano har da ta Tudunwada inda aka kwantar da mutane a asibiti.

Kawo yanzu kimanin mutane goma ne ke kwance a babban asibitin garin Tudunwada suna karbar magani.

Banda wadan nan akwai wasu kuma suna karbar maganin suna komawa gida.

Sauran kananan hukumomin da aka samu barkewar cutar sun hada da Doguwa da Garko da Gaya da Wudil da Dawaikin Kudu da Rano da Sumaila da kuma karamar hukumar Kabo.

Abdullahi Iliyasu Riyasa wakilin mazabar Tudunwada a majalisar dokokin jihar Kano ya tabbatar da bullar cutar a wasu kauyuka dake cikin karamar hukumar ta Tudunwada. Ma'aikatar magani ta karamar hukumar ta dauki magani ta shiga duk kauyukan da suka kamu da cutar. Haka kuma ana bayar da maganin riga kafin kamuwa da cutar. Sakamakon bullar ciwon an samu wadanda suka rasu.

Dan majalisar ya danganta bullar cutar da yanayin damuna da ake ciki yanzu. Yace yawancin ruwan rijiyoyi da mutane ke sha sun samu gurbata sabili da ambaliyar ruwan sama. Amma yace an samu magunguna da za'a saka cikin rijiyoyin da kuma tsaftace ruwan da suke sha.

Dangane da samar da ruwan famfo dan majalisar ya amabaci wuraren da aka riga aka sa famfao kuma ana cigaba da shirin samarma wasu wuraren.

Kananan hukumomi tare ne dai suka kamu da cutar.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kawari.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Kwalara Ta Barke a Karamar Hukumar Tudunwada Jihar Kano -2' 45"