Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Na Yiwa 'Yan Siyasa Kaimi Su Guji Rikicin Zabe


gwamnatin Najeriya ta bukaci 'yan siyasa su yi watsi da rigingimun zabe
gwamnatin Najeriya ta bukaci 'yan siyasa su yi watsi da rigingimun zabe

Mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara a kan jam'iyu, sanata Ben Obi ne ya fadi haka

Gwamnatin tarayyar Najeriya na kira ga 'yan siyasa da su guji rigingimu da tashe-tashen hankula masu alaka da zabe.

Mashawarcin shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan na musamman akan harakokin jam'iyun siyasa, Sanata Ben Obi ne ya furta hakan a birnin Osogbo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Sanata Ben Obi ya je Osogbo ne domin halartar wani taron bita da aka shirya domin fadakar da jam'iyun siyasa ishirin da za su tsaida 'yan takarar neman gwamnan jahar Osun a zaben da za a yi ranar tara ga watan takwas a shekarar nan ta dubu biyu da goma sha hudu.

Wakilin Sashen Hausa a shiyyar Hassan Umaru Tambuwal ne ya hada rahoton.

XS
SM
MD
LG