Da Alamu Akwai Matsala Tsakanin APC Da CPC

Tambarin jam'iyyar APC

Bisa ga alamu akwai matsala tsakanin sabuwar jam'iyya da bangaren CPC da yake cikin hadakar da ta haifi APC.
Duk da murnar da 'yan jam'iyyar CPC ke yi cewa sabuwar jam'iyyar hadaka ta APC an yi mata rajista suna cike da korafe- korafe.

Abokin aiki Aliyu Mustapha ya zanta da Alhaji Dan Bilki, daya daga cikin kusoshin jam'iyyar CPC dake cikin hadakar sabuwar jam'iyyar APC. A firarsu ya godewa Allah sun samu ragista to amma da walakin. Ya ce matukar shugabanni ba zasu tsaya don Allah ba suna nuna wariya to ko gidan jiya aka koma.

Yayin da yake amsa tambayar ko akwai wata matsala a kasa yanzu sai ya ce akwai. Ya ce bai kamata a yi tafiya irin ta da ba kara zube. Ya ce idan da jam'iyyar CPC ta Janaral Buhari ce to yanzu jam'iyyu uku suka hade suka haifi APC lamarin da ya mayarda ita jam'iyyar kowa da kowa.Idan ana son a fitar da Najeriya daga irin halin da ta shiga yanzu to dole ne akai zuciya nesa a sa jam'iyyar APC da Najeriya gaba ba son kanmu ba kamar yadda alamu ke nunawa yanzu.

Da yake bada amsa game da abubuwan dake faruwa yanzu ya ce da aka tashi zaban shugabannin riko na jam'iyyar APC sai aka yi watsi da mutanen Janaral Buhari su goma sha daya. Ba'a ba kowa cikinsu ba wani mukami sai wata mace daya. Ya ce a cikin shekaru goma sha daya da Janaral Buhari ya shiga siyasa suna bisa tun daga ANPP har zuwa kafa CPC. Ya ce yakamata a tsaya kan dimokradiya ba kan fadanci ba. Wadanda suka iya fadanci su ne aka sa kan gaba su zama shugabannin riko na kasa na sabuwar jam'iyyar.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Da Alamu Akwai Matsala Tsakanin APC Da CPC - 4:00