Accessibility links

Rajista Ma APC Zata Tsarkake Siyasar Najeriya In Ji Samuel Lalong


Tambarin APC

Tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Filato yace rashin adalci da zalumcin PDP su suka haifar da sabuwar jam'iyyar APC

Tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Filato, Samuel Lalong, yace rajistar da hukumar zabe ta Najeriya, INEC, ta yi ma sabuwar jam'iyyar nan ta APC, ba karamin taimako zai yi ba ga tsarkake harkokin siyasar Najeriya.

A cikin hirar da yayi da Aliyu Mustapha, Mr. Lalong yace wannan rajistar an jima ana jiran a ganta, kuma da ba a yi ba, to bai san abinda zai faru ba. Yace dalilin wannan kuwa shi ne jam'iyyar dake mulkin Najeriya, PDP, ta nuna cewa ba siyasa ake yi a kasar ba, kuma babu adalci a harkar mulki.

Barrister Lalong yace idan kuwa babu adalci a cikin siyasar kasa, dole ne a samu wanda zai nuna adalci, yana mai fadin cewa akasarin wadanda suka hadu suka kafa wannan jam'iyya ta APC mutane ne da aka sansu da gaskiya, wadanda kuma sun yi jam'iyyar PDP, amma rashin gaskiyarta ya kore su.

A kan ko wadanda suka hadu suka kafa APC zasu iya tafiyar da ita ba tare da an samu sabanin ra'ayi ba, Lalong yace ai tun farko ma an zaci cewa haduwar jam'iyyun ba zata iya kawowa wannan matakin ba, amma ga shi yau sun zamo daya.

Yace ganin komai yana lalacewa a Najeriya, siyasa ta zamo abar yin gori, PDP ta zamo azzaluma, har ma tana iya korar wasu daga cikinta saboda tana ganin ta isa, ba a bin doka, tilas ne a samu wata madafar da masu mutunci da gaskiya zasu iya dogaro kanta.

XS
SM
MD
LG