Dakarun da ke adawa da Gaddafi a Libiya sun abka cikin Bani Walid

  • Ibrahim Garba

Wasu dakarun 'yan tawaye a wajen garin Bani Walid

Dakarun gwamnatin wuccin gadin Libiya, sun abka cikin garin Bani Walid

Dakarun gwamnatin wuccin gadin Libiya, sun abka cikin garin Bani Walid da ke cikin Hamada, inda hakan ya fadda girman farmakin da su ke kaiwa kan ‘yan wuraren das u ka rage a hannun Gaddafi.

Shaidu a wurin sun ce an yi ta jin kararrakin tashe-tashen bama-bamai da aman bindigogi a dukkannin sassan garin a yau Jumma’a, a sa’ilinda dakarun nan Gwamnatin wuccin gadin su ka gamu da turjiya mai tsanani daga dakarun Gaddafi.

Wannan fantsama cikin garin Bani Walid ta faru ne kwana guda bayan da dubu dubatan mayakan ‘yan tawaye sun kutsa cikin tsakiyar garin haihuwar Gaddafi wato Sirte.

Jami’an sojojin ‘yan tawayen sun ce sun fuskaci martani mai tsanani daga sojojin musamman da kuma sojojin da ke labe; kuma rahotannin kafafen yada labarai sun ce har zuwa yau Jumma’a ana ta tabka fada.