Accessibility links

Dakarun da ke adawa da Gaddafi sun gamu da turjiya a Bani Walid da Sirte

  • Ibrahim Garba

Wasu daga cikin dakarun da ke adawa da Gaddafi a kusa da Sirte

Dakarun gwamnatin wuccin gadin Libiya, na ta kokarin dannawa cikin sauran

Dakarun gwamnatin wuccin gadin Libiya, na ta kokarin dannawa cikin sauran wuraren da su ka rage a hannun tsohon Shugaban Libiya Moammar Gaddafi, a sa’ilinda yawan kasashen duniya da ke bayar da goyon baya ga gwamnatin wuccin gadin keta karuwa.

Dakarun gwamnatin wuccin sun kai mamaya a garin Bani Walid, da ke cikin Hamada, inda suka shiga fafatawa sosai da magoya bayan Gaddafi har rahotanni ke nuna cewa suna janyewa daga tsakiyar birni. Haka zalika sun fuskacin tsananin turjiya daga magoya bayan Gaddafi a Sirte, garin haihuwar tsohon Shugaban. Shaidu sun ce jiragen NATO sun yi ta shawagi bisa Sirte a daidai lokacin da ake ta jin kararrakin bindigogi da harbe-harben manyan rokoki akai-akai a wannan gari da ke gabar tekun Mediterranean da ya game da hayaki.

Rahotanni daga Bani Walid na nuna an yi barin wutar gaske. Kamfanin dillancin labaran Reuters y ace dakarun gwamnatin wuccin gadin sun ma janye daga tsakiyar garin.

Fafatawar ta yau Jumma’a farkon wani zango ne na fadada farmakin da dakarun gwamnatin wuccin gadin ke kai wa kan sauran wuraren da su ka rage a hannun Gaddafi.

A daidai lokacin da dakarun gwamnatin wuccin gadin ke kara cimma dakarun Gaddafi, Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar bayar da kujerar kasar Libiya da ke babban sauran taro ga Majalisar Shugabancin Wuccin Gadin kasar.

An kai ga amincewa da hakan ne da kuri’u 114 na goyon baya da kuma 17 na kin amincewa da kuma 15 na kauracewa; wanda hakan ya baiwa Majalisar Shugabanci Wuccin Gadin damar nada Jakada kafin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi mako gobe.

XS
SM
MD
LG