Spain: Danbarwar Siyasa a Catalonia Ta Dau Sabon Salo

Dubban masu zanga-zangar a yankin Catalonia sun hau kan tituna tare da rufe filin jirgin saman Barcelona a jiya Litinin, bayan da Kotun Kolin Spain ta yankewa shugabannin ‘yan aware hukuncin zaman gidan yari mai tsawo, saboda yunkurinsu na ayyana ‘yancin kai daga Spain a shekarar 2017.

Masu zanga-zangar sun toshe kofar shiga filin jirgin saman El Prat na yankin, abin da ya janyo 'yan sandan kwantar da tarzoma suka hau kansu da kulakai.

Jami’an kiwon lafiya sun ce masu zanga-zangar 37 sun samu raunuka a rikicin da aka yi a tashar jirgin sama. Sannan aka soke akalla zirga zirgar jirage 108 , a cewar jami’an filin tashin jirgin.

Wasu 'yan siyasar Catalan da muka zaba a cikinsu za su yi abin da suke so su yi. Kuma sun je kurkuku don san ranmu, don zaɓin demokraɗiyya da siyasa na son gudanar da zaɓe. Saboda haka, an yanke musu hukuncin ɗaurin kurkuku tare da hukuncin da ba su dace ba, a cikin hukuncin da za ta kunyata kowa da duk wata ma'anar dimokiradiyya."