Daukar Sabbin Matakai Kan Sarkin Kano Ba Dai-dai Bane - Bafarawa

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Na Biyu Da Ayarinsa Ranar Juma'a A Kano

Tsohon gwamnnan jihar Sokoto, Attahiru Dalahatu Bafarawa, ya ce ‘daukar sabbin matakai kan mai martaba sarkin Kano Sanusi bayan sulhu da gwamnoni suka yi kan lamarin a Kaduna ba dai-dai ba ne.

Bafarawa da ke magana da manema labarai a Abuja, ya ce karin mataki ko neman kwabe sarkin zai rage darajar sarauta ne da hadin kan arewa. Yace “abin kunya ne garemu ‘yan arewa ace yau a Majalisar jihar Kano ana binciken sarkin Kano.”

Ya ci gaba da cewa idan har gwamnonin arewa su hudu zasu je su zauna da gwamnan Kano, kuma sarkin Kano a gwada masa irin kura-kuransa har ya yarda, sai a bari a ga alkawarin da yayi zi cika inji Bafarawa.

Majalisar dokoki ta jihar Kano dai ta kafa kwaitin bincike akan mai martaba Sarkin Kano da majalisar Masararutar Kano, game da zargin kashe kudade ba tare da amincewar ita majalisar ba.

Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Daukar Sabbin Matakai Kan Sarkin Kano Ba Dai-dai Bane - Bafarawa - 2'52"