Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu Hukumomi Biyu Ne Ke Binciken Sarkin Kano


Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi ll
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi ll

Binciken da majalisar dokokin Kano ta kaddamar jiya kan masarautar Kano kari ne akan wanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ko EFCC reshen Kano ta keyi bisa zargin barna da dukiyar jama'a da aka ce masarautar tayi tun daga lokacin da sarki mai ci yanzu ya hau karagar mulki

Baicin zargin da ake yi masa da yin watanda da kudade ana kuma zarginsa da shiga harkokin siyasa da aiwatar da wasu ayyuka da suka ci karo da al'adun fada wadanda suke cikin zargin da majalisar dokokin jihar ta yiwa sarkin.

To amma Malam Ibrahim Ado Kurawa masanin tarihi da ayyuka da ka'idojin fadar Kano na cewa a matsayin Sarki Muhammada Sanusi ll na masanin tattalin arziki duk duniya na gayyatarsa ya gaya masu yadda zasu gyara abubuwa. Shin idan an nemeshi ya taimaka da gyara sai ya ki?

Yace mutanen arewa suna bashi mamaki. Lokacin da ake rigingimu an soki sarakunan da rashin cewa komi. Yanzu Sarki Sanusi yana fadan abubuwan da aka yi ba daidai an ce yayi laifi.

Yana mai cewa Sarki shi ne fada. Duk abun da ya ga dama zai yishi. Abu daya ne ba zai yi ba shi ne ya yiwa Allah sabo. Yace sabo da haka mutane su daina cewa sarki ya sabawa abun da ake yi a fada.

Yanzu dai hukumomi guda biyu ne ke gudanar da bincike akan aikata ba daidai ba da ake zargin Sarkin Kano da yi.

Barrister Audu Bulama Bukarti na tsangayar aikin lauyoyi dake Jami'ar Bayero ta Kano yayi tsokaci ta fuskar shari'a.

Yace dokar kasa ta ba hukumomin dake binciken sarkin su bincikeshi idan har an yi wani abu da ba daidai ba musamman wajen kashe kudaden al'umma. Sai dai yace abun duba shi ne yaya za'a ce hukumomi biyu na bincike akan abu daya. Yace dokar da ta kafa EFCC ba zata bari ta cigaba da binciken ba domin wata hukuma ta shigo. Kwamitin binciken majalisar dokoki na 'yan siyasa ne kuma babu yadda ba za'a shigo da batun siyasa ciki ba.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG