Dawo Da Zaben Fidda Gwani Hannun Hukumar Zabe Ne Mafita - Tsohon Darakta Kabiru Adamu

INEC

Ma'abota lamuran zabe da siyasa na cewa dawo da hakkin gudanar da zaben fidda gwani hannun hukumar zabe ne zai gyara harkar dimokradiyya a Najeriya.

A sharhin masanan, wannan zai ba da dama mutanen da ke da goyon bayan jama'a ba jami'an jam'iyya ba za su samu damar yin takara da lashe zabe.

Kamar yanda a ke kira ga mika gudanar da zaben kananan hukumomi ga hukumar zabe ta kasa INEC, haka ma batun zaben fidda gwani ya zama muhimmin batu don yanda takaddamar da ke sa kotuna rushe zabe bayan wasu sun lashe kamar yanda ya faru a Zamfara inda Shehu Mukhtar Kogunan Gusau ya rasa kujerar gwamna, hakanan Celestine Omehia ya bar fadar gwamnatin Ribas aka rantsar da tsohon gwamna Rotimi Amaechi.

Karin bayani akan: INEC, APC, PDP, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A Bayelsa Douye Diri na PDP ya tsinci dami a kala bayan kotu ta hana rantsar da David Lyon na APC. Hope Uzodinma ya zama gwamna a Imo duk da shi ya zo na hudu a yawan kuri'u ya sa dole Emeka Ihedioha ya kwashe kayan sa daga fadar gwamnati a Owerri.

Tsohon darakta a hukumar zabe sarkin tafarkin Bauchi Kabiru Adamu ya ce amshe ikon zaben fidda gwanin 'yan takarar jam'iyyu zai kawo maslaha.

Ita kuma malamar jami'a a Itas Gadau Dr. Furera Bagel na nuna tamkar a na gaggawa ne wajen gwada dimokradiyyar Najeriya da kasashen duniya da su ka dade a cikin ta.

Babban zaben Najeriya na zuwa a 2023, inda shugaba Muhammadu Buhari ke fatar APC tazarce don manufofi irin na gwamnatin sa su dore, yayin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke arar logar kamfen din Buhari wato "Jiki Magayi."

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Dawo Da Zaben Fidda Gwani Hannun Hukumar Zabe Ne Mafita - Tsohon Darakta Kabiru Adamu