Dillalan Agushi Na Samun Riba A Kudancin Najeriya

Dillalan agushi daga arewacin Najeriya sun ce, yanzu haka cinikin agushi na kara armashi a kudancin kasar, sakamakon gagarumar ribar da suke samu a sassan yankin, yayin da suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar musu tallafi, ta kuma dauki kwakkwaran mataki wajen magance yawan haraji akan hanyoyin jihar Benue.

Malam Ibrahim Sa'id, wanda aka fi sani da Babangida Ikom, wani dillali ne da ke fataucin agushi daga jihar Taraba zuwa jihar Imo. Ya yi bayani kan cinikin agushi da yadda lamarin yake a yankin kudu a halin yanzu, da kuma wasu kalubalen da harkar ke fuskanta.

Haka zalika, wasu dillalai sun bayyana yadda lamarin yake.

Bayanai daga masana da manoma da dillalai na nuni da cewa agushi bai bukatar ruwa sosai, saboda nomansa ya fi bunkasa ne a lokacin rani.

A yammacin Afirka, Najeriya ce ke noma kashi 65 cikin 100 na agushi, kuma an fi samun wadatarsa a jihohin arewa kamarsu Taraba, Benue, Nasarawa da kuma Kogi, kamar yadda binciken shafin finelib.com ya nuna.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe.

Your browser doesn’t support HTML5

Dillalan Agushi Na Samun Riba A Kudancin Najeriya