DOMIN IYALI: Cin Zarafin Iyali A Cikin Gida Kashi Na Daya -Afrilu 29, 2021

Alheri Grace Abdu

A ci gaba da haska fitila kan rahotannin cin zarafin da tashin hankali a tsakanin iyali a jihar Naija inda wata mata ta kashe kishiyarta sabili da kishi, da kuma magidanci da ya kashe matarsa bayan wata rashin jituwa, mun gayyaci masu ruwa da tsaki da nufin neman hanyar shawo kan wannan matsala.

Bakin da madugun tattaunawar Mustapha Nasiru Batsari ya gayyata domin neman hanyar warware zaren sun hada da: Alh Bello Sheriff, Shugaban Kungiyar matasan Najeriya reshen jihar Naija, da Mohammed Sa'idu Etsu, shugaban kungiyar inganta rayuwar matasa a jihar Naija, da kuma Barista Hadiza Nura Alfa, Lauya da ke kungiyar kare hakkokin mata WRAPA a jihar Naija,

Saurari kashin farko na tattaunawar:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Cin Zarafin Iyali A Cikin Gida Kashi Na Daya-10:"