Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Cin Zarafin Iyali A Cikin Gida -Afrilu 15, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Alkaluma na nuni da cewa, an sami karuwar cin zarafin al'umma da kuma tashin hankali a tsakanin iyali a cikin shekara guda da ta shige da aka fuskanci barkewar annobar korona da ta tilasta takaita zirga zirga ta kuma sauya yadda aka saba rayuwar yau da kullum.Wannan lamari ya shafi dangantaka tsakanin iyaye da 'ya'yansu da kuma ma'aurata da ya kai ga rasa rayuka.

A yau shirin Domin Iyali ya fara haska fitila kan lamarin da ya auku a baya bayan nan a jihar Naija da ya kai ga asarar rayukan mata biyu a gidajen aure dabam dabam.

Saurari bayanin Mustapha Nasiru Batsari kan inda aka kwana dangane da matar da ta kashe kishiyarta sabili da kishi, da kuma magidancin da ya kashe matarsa bayan wata rashin jituwa.

DOMIN IYALI:Cin Zarafin Iyali A Cikin Gida-10:00""
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:19 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG