DOMIN IYALI: Matsayin Matasa Kan Matsalar Fyade A Najeriya- Kashi Na Daya, Yuni 25, 2020

Alheri Grace Abdu

A yau shirin Domin Iyali ya gayyaci matasa domin tofa albarkacin bakinsu a yunkurin da ake yi na shawo kan matsalar fyade da ta buwayi al’umma a Najeriya, abinda ya sa mata gudanar da zanga zanga a birane da dama na kasar.

Wannan lamarin ya sa aka kakkafa kungiyoyin fafatuka da tada tsimin al’umma a matakai daban daban.

Matasan da wakiliyarmu Baraka Bashir ta tattauna da sun sune Zainab Nasir Ahmed, Salim Wada Usman, Ibrahim Bala, Safiya Daba, Zilahayuwas Danjuma.

Saurari shirin domin jin kungiyoyin da suke wakilta da kuma yadda suke kallon lamarin.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa Sun Yi Tsokaci Kan Fyade A Najeriya: PT1-10:00"