Dubai Ta Yi Umarnin Rufe Asusun 'Yan Najeriya

Shugaban Daular Larabawa, Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum

Hadaddiyar daular larabawa sun bada umarnin a rufe dukfan asusun ‘yan Najeriya da suke kasashensu kamar su Dubai da makamantansu.

Dalilin da yasa hakan ya faru shine, daular Larabawan ta bada bayanin cewa, sun lura da cewa akwai hada-hadar kudaden haram da wasu ‘yan Najeriyar ke yi ta hanyar fakewa da maganar aikawa ‘ya’yansu dake karatu kudade a kasashen Larabawan.

Wani masanin harkokin bankuna ya bayyana yadda abin yake, inda yace ta yiwu akwai harkokin da suke yi da basu kamata ba ne da suka taka doka ko kuma tababar yawan kudin da kuma inda suka fito, kila shi ne yasa suka ware ‘yan Najeriya kawai a wannan umarni.

Sannan kuma ya kalli abin ta fuskar kasar Najeriya da cewa gwamnati mai zuwa tana iya hada kai in tana so da irin wadannan kasashen da ake jidar kudaden kasa ana kaiwa ana boyewa a can. A hirar tasa da Jummai Ali ta Muryar Amurka, ya bada misalin cewa hakan yana iya taimakawa tattalin arzikin kasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Dubai Ta Yi Umarnin Rufe Asusun 'Yan Najeriya - 1'48"