Accessibility links

Yarjejeniyar Zaman Lafiya a Afirka Ta Tsakiya


Shugabar kasar Afirka ta Tsakiya ta wucin gadi Catherine Samba-Panza

Gwamnatin kasar Afirka ta Tsakiya da wasu kugiyoyi goma masu makamai sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya a karkashin wani shiri na majalisar dinkin duniya

Gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da kungiyoyi masu dauke da makamai goma sun sa hannu a yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya jiya Lahadi da zumar kawo karshen kazamin fadan da aka yi tsawon shekaru biyu ana yi da ya yi sanadin kashe dubban mutane.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Babacar Gaye yace, “Na hakikanta cewa, da gaske suke, zamu kuma maida hankali wajen ganin an sami zaman lafiya mai dorewa”.

Masu shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya sun ce, duka bangarorin sun amince da ajiye makamai, da daina amfani da bindiga wajen warware rikicin dake tsakaninsu, da kuma daukar matakan ajiye makamai da daina gayyar mayaka da kuma sake shiga al’umma, da tsugunarwa.

Yarjejeniyar ta kuma kunshi haramta shigar da kananan yara aikin soja ko kuma bautar da su.

‘Yan tawaye Musulmi sun kwace Bangui babban birnin jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a cikin shekara ta dubu biyu da goma sha uku, da ya haifar da kazaman hare hare da ramuwar gayya tsakanin mayaka Kirista da Musulmai.

Duk da yake ana samun tashin hankali loto-loto, an sami kwanciyar hankali karkashin jagorancin shugabar wucin gadi Catherine Samba-Panza, wadda keda goyon bayan dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

XS
SM
MD
LG