Duk Da Fenaritin Da Ya Zubar, Messi Ne Zakaran Kwallon Kafa Na Duniya – Xavi Hernandez

Lionel Messi

Messi ya zubar da bugun ne a daidai lokacin da wasa ya yi zafi kuma babu wani bangare da ya zura kwallo a raga.

Mai horar da ‘yan wasan Barcelona, Xavi Hernandez, ya ce duk da cewa Lionel Messi ya barar da bugun fenariti a wasan PSG da Real Madrid, shi ne zakaran kwallon kafa na duniya da tarihi ba zai manta da shi ba.

A ranar Talata Messi ya zubarwa da PSG bugun fenariti a zagayen 16 a wasan UEFA yayin da suke karawa da Real Madrid da ta kai musu ziyarar a Paris.

Messi ya zubar da bugun ne a daidai lokacin da wasa ya yi zafi kuma babu wani bangare da ya zura kwallo a raga.

“A matsayinsa na wanda yake bugawa PSG wasa a kuma matsayinsa na Messi, ba abin mamaki ba ne idan mutane suna sukar shi. Ni ina mai fatan alheri, saboda abokina ne. Ya ba da gagarumar gudunmowa ga Barcelona, a wurina, babu haufi, shi ne dan wasa mafi kwazo a tarihin kwallon kafa.” In ji Hernandez.

PSG dai ta yi nasarar lashe wasan da ci 1-0 bayan da Kylian Mbappe ya zura kwallo a ragar Madrid ana gab da tashi a wasan.

Wannan labari ne daga kamfanin dillancin labarai na AP wanda Mahmud Lalo ya fassara.