Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PSG Za Ta Sayar Da ‘Yan Wasa Bakwai Don Ta Biya Messi 


Messi a lokacin wasansu da Reims

PSG na kashe euro miliyan 300 wajen biyan daukacin tawagar ‘yan wasanta inda Messi dan shekara 34 yake daukan miliyan 41 a shekara.

A wani yunkuri na ganin ta samu kudaden da za ta rika biyan dan wasanta Lionel Messi, kungiyar Paris Saint Germain ta kasar Faransa na shirin sayar da ‘yan wasa bakwai.

Wannan mataki ne da zai ba kungiyar damar tattaro kudaden domin sauke nauyin biyan Messi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Rahotannin sun ce kungiyar za ta yi amfani da kasuwar cinikin ‘yan wasa da za a bude a watan Janairu don sayar da ‘yan wasan.

A watan Agusta Messi ya koma kungiyar ta PSG bayan da Barcelona ta gaza hada kudaden biyansa.

Ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu da PSG, akwai kuma yiwuwar a kara sabunta kwantiragin da karin shekara daya.

Rahotanni sun ce ana biyan Messi euro miliyan 41 a shekara hade da kudaden alawus-alawus.

PSG na kashe euro miliyan 300 wajen biyan daukacin tawagar ‘yan wasanta inda Messi dan shekara 34 yake daukan miliyan 41 a shekara.

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG