DUNIYAR AMURKA: Amurka Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Ukraine Duk Da Rikicin Isra’ila Da Hamas, 01 Disamba, 2023

Mahmud Lalo

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya sake komawa Isra’ila, inda zai sake neman a kara tsawaita yarjejeniyar dakatar da bude wuta saboda a sake fadada damar sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza a kuma kara shigar da kayayyakin agaji cikin yankin.

Hakan na faruwa ne bayan da Blinken ya kara jaddada goyon bayan Amurka ga Ukraine yayin da hukumomin kasar ke shirin fafatawa a daidai lokacin da aka tunkari yanayi na hunturu.

Your browser doesn’t support HTML5

DUNIYAR AMURKA: Amurka Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Ukraine Duk Da Rikicin Isra’ila Da Hamas - 5'45"