Eric ten Hag Ya Shiga Wembley Da Kafar Dama

Wasan Karshe Na Kofin Carabao - Manchester United da Newcastle United

Kungiyar Manchester United na murnar lashe gasar cin wani babban kofi a karon farko a karkashin kocinta Erick ten Hag bayan da ta doke Newcastle a wasan karshe da suka yi na cikin kofin Caraboa.

Bangarorin biyu dai sun shiga wasan kowannensu na kokarin samun nasara ido rufe, wacce za ta iya samar da kyakkyawar makoma, kuma 'yan wasan Manchester United da ke kara gogewa ne suka samu narasa.

Kungiyar United ba ta ci wata kyautar azurfa ba tun 2017, kuma ta kawo karshen gaza cin kofi a tsawon shakaru 40 bayan da ta doke Newcastle da ci 2-0 a filin wasa na Wembley, inda Casemiro ya zura kwallo da ka shi kuma Sven Botman ya ci gida.

Wasan Karshe Na Kofin Carabao - Manchester United da Newcastle United

Karshen wasan ya yi wa 'yan wasan Newcastle zafi sosai a karon farko da suka kai wasan karshe tun lokacin da Manchester United ta ci su 2-0 a wasan cin kofin FA Cup na 1999.

Ta yiwu da abubuwa sun bambanta ga 'yan wasan Eddie Howe in da ba a ankarar da David De Gea hana Allan Saint-Maximan damar harba kwallo a kusa-da-kusa a karshen zagayen wasan na farko.

Mai tsaron gida na uku, wanda wannan shi ne wasansa na farko a cikin kwanaki 728, ya dakile kwallon da Wout Weghorst ya yi niyar zurawa a wasan da zai basu nasara a mintunan karshen na rabin lokaci.

Wasan Karshe Na Kofin Carabao - Manchester United da Newcastle United

‘Yan wasan Newcastle sun dawo daga hutun rabin lokaci da karsashi amma suka kasa tabuka abun kirki, lamarin da zai tsawaita musu lokaci na cin wani kofi karon farko tun bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin Inter-Cities Fairs a shekarar 1969.

Ga su wadanda suka yi nasara kuma, a wasan Ten Hag karon farko a Wembly ya hada shi da Jose Morinho a matsayin kocin United na farko da ya lashe wani babban kofi a kakar wasansu na farko.