Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Edinson Cavani Ba Zai Buga Wasansu Da Atletico Madrid Ba


Edinson Cavani

Baya ga wasan na Atletico da United, Benfica za ta karbi bakuncin Ajax a wasa na biyu da za a buga a wannan Laraba.

Dan wasan Manchester United Edinson Cavani ba zai buga wasan farko na zagayen ‘yan 16 da za su kara da Atletico Madrid ba.

A ranar Larabar nan Atletico za ta karbi bakuncin United a wasan gasar UEFA Champions League.

Mai horar da United Ralf Rangnick ta tabbatar da cewa dan wasan na na fama da jinya, saboda haka ba da shi za a je kasar ta Sifaniya ba.

A baya, masu sharhin kwallon kafa sun nuna yiwuwar haduwar gwarazan kwallon kafar Uruguay biyu da za su kara a bangarorin biyu, wato Luis Suarez na Atletico da Cavani a bangaren United.

Amma ga dukkan alamu wannan haduwa ba za ta yi wu ba.

Baya ga wasan na Atletico da United, Benfica za ta karbi bakuncin Ajax a wasa na biyu da za a buga a wannan Laraba.

A wasannin da aka buga a ranar Talata, Villareal da ta karbi bakuncin Juventus, inda suka tashi da ci 1-1.

Chelsea kuma ta doke Lille ta kasar Faransa da ci 2-0 a Stamford Bridge.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG