Euro: Bukayo Saka Ya Nemi Afuwa, Ya Maida Martani Ga Masu Sukar Shi

Kocin Ingila Southgate yana rarrashin Saka bayan da ya barar da fenariti

Dan wasan Ingila Bukayo Saka ya nemi afuwar al’umar kasar Ingila saboda fenaritin da ya zubar a wasan karshe na gasar cin kofin Euro 2020 da suka kara da Italiya.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, Saka ya ce ba zai iya misalta yadda ya ji ba bayan da ya gaza cin fenaritin.

“Babu kalaman da za su iya nuna yadda na ji kan fenaritin da na buga. Ku yi hakuri mun gaza kawo maku kofin gida a wannan shekara.

“Amma na yi maku alkawari za mu yi iya bakin kokarinmu mu ga cewa al’umar wannan zamani (ta Ingila) ta dandana yadda dadin nasara take.” In ji Saka.

Marcus Rashford da Jadon Sancho, sun bararwa da Ingila fenariti a wasan karshe da kasar ta buga da Italiya a ranar Lahadi, sai dai wacce Saka ya buga ta karshe, ita ta ba Italiya nasarar ta lashe kofin.

Hakan ya sa jama’a da dama suka yi ta sukar su da furta kalaman wariyar launin fata a shafukan sada zumunta. Duka 'yan wasan uku bakaken fata ne.

Hukumomin kasar sun yi ta Allah wadai da masu sukar su, inda har Firai Ministan ingila Boris Johson ya fito ya yi tir da masu sukar nasu.

Ko da yake, an samu wasu dama sun fito sun nunawa ‘yan wasan goyon baya.

“Ina mika godiyata ga wadanda suka yi ta fafutukar a madadi na da wadanda suka aiko min da iyalina wasikun rarrashi. Haka ya kamata a ce ana wasan kwallo.”