Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EURO 2020: Wa Zai Kai Ga Gaci, Ingila Ko Italiya?


Tambarin karawar Ingila, dama da Italiya, hagu

Ingila da Italiya na shirin karawa a ranar Lahadi a wasan karshe na gasar Euro 2020 bayan da suka yi nasarar lashe wasanninsu na semi-final.

Italiya ta doke Sifaniya ne yayin da ita kuma Ingila ta yi waje da Denmark, nasarorin da suka ba su damar kai wa gurbin wasan karshe.

A fitaccen filin Wembley da ke London a Ingila za a buga wasan.

Tuni masu sharhi a fagen kwallon kafa suka fara dora wannan karawa a ma’aunin karfi da raunin da kungiyoyin biyu suke da shi.

Ita dai Italiya an san ta da yin fice a fannin iya tsare tsakiyar filin wasa.

Dan wasan tsakiyar Italiya, Marco Verratti, na daga cikin fitattun ‘yan wasan tsakiya a duniya, baya ga haka ga Nicola Barella mai shekara 24, wanda matashi ne sai kuma Jorginho.

Wadannan ‘yan wasa uku kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito sun kware wajen iya rike tsakiyar fagen wasa, dalilin da ya sa Roberto Mancini ya zabi zuwa da su gasar.

Ita kuwa Ingila ta fi karfi ne wajen masu kai hari a daukacin gasar, abin da zai taimaka mata musamman idan har wasan ya kai ga karin lokaci.

Irin ‘yan wasan da Ingila ke da su ajiye a benci, na daga cikin karfin da take da shi.

‘Yan wasa irinsu Jordan Henderson da Phil Foden na daga cikin babban jarin da Ingilar take da shi idan Gareth Southgate ya tashi yin canji.

Sai dai dukkan kungiyoyin biyu na da nasu raunin idan aka duba wasannin baya da suka buga.

Misali, mai tsaron Ingila Jordan Pickford, na daya daga cikin ‘yan wasa da kungiyar ta fi nuna damuwa akansu a lokacin zuwa gasar.

Ko da yake, bai fuskanci wani kalubale ba a wasannin da suka yi a baya, amma a wasan Ingila da Denmark, Pickford ya nuna rauninsa, musamman yadda yake doka kwallo.

Italiya a nata bangaren kamar yadda watakila Ingila ta lura, mai tsaron gidanta na bangaren hagu Emerson Palmeiri ya yi ta bari ‘yan wasan Sifaniya suna ta wuce shi a karawarsu.

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG