Fadar Shugaban Najeriya Ta Yi Watsi Da Barazanar Nnamdi Kanu

Shugaban 'yan aware na kungiyar fafutukar kabilar Igbo IPOB, Nnamdi Kanu

“Fadar shugaban Najeriya, karkashin jagorancin shugaba Muhammad Buhari na da karfin da za ta kare kan iyakokin kasar daga duk wata barazana.”

Fadar shugaban Najeriya ta yi wancakali da barazanar da shugaban kungiyar ‘yan aware ta Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu ya yi, inda ya ke cewa zai dawo gida ya ci gaba da fafutukarsa ta ganin an raba kasar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mai bai wa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkar yada labarai, Malam Garba Shehu, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi biris da kalaman na Kanu.

“Fadar shugaban Najeriya, karkashin jagorancin shugaba Muhammad Buhari na da karfin da za ta kare kan iyakokin kasar daga duk wata barazana.” Inji sanarwar.

A karshen makon da ya gabata, Kanu, wanda rabon da a ji duriyarsa tun a watan Satumbar bara, ya bayyana a wani faifan bidiyo yana barazanar ta da hankali a kasar idan ba a raba yankin kabilar Igbo da sauran sassan kasar ba.

Bidiyon ya nuna yadda Kanu a kasar Isra’ila, amma kuma hukumomin kasar sun ce bai shiga kasar ba, suna masu cewa ta iya yiwuwa tsohon bidiyo ne.

Bayan hakan ne kuma ya bayyana shafin Facebook na kungiyar ta IPOB a ranar Lahadi yana mai barazana ga hukumomin Najeriyar.

Sai dai sanarwar gwamnatin Najeriya ta fitar ta bayyana kurarin na Kanu a matsayin mara tushe.

“Muna kallon wannan barazana a matsayin wani shiri na dauke hankalin (gwamnati) wacce ba za ta yi nasara ba wajen katse dangantakar Najeriya da sauran kasashen duniya.”

Sanarwar ta kara da cewa, Najeriya na ci gaba da tuntubar kasashen da take hulda da su, “kuma sun ba mu tabbacin cewa za su ci gaba da mutunta Najeriya a matsayin kasa dunkulalliya.

Bacewar Kanu a watan Satumbar bara yayin wata arangama da aka yi tsakanin dakarun Najeriya da magoya bayansa a jihar Abia, ta haifar da zargin cewa an kashe shi ne ko kuma hukumomi na tsare da shi.