Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakatar Da Babban Sakataren Hukumar Lafiya Ta Najeriya


 Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Shugabar hukumar darektocin harkokin kula da lafiya ta Najeriya ta sanar da dakatar da babban sakataren hukumar bisa zargin wuce makadi da rawa, bayan irin wannan dakatarwa a baya da binciken da shugaba Buhari ya kaddamar ya wanke shi.

Shugabar hukumar daraktocin hukumar lafiya ta Najeriya Dakta Iyantu Ifenna ta bada sanarwar dakatar da babban sakataren hukumar Farfesa Usman Yusuf har sai illa masha Allahu bisa abin da ta kira rashin bin ka'idoji da wuce gona da iri da yake yi da baza a iya kauda kai daga garesu ba.

Hukumar daraktocin ta yanke shawarar kafa kwamitin bincike domin gano abubuwan da suka faru, kuma an ba wannan kwamiti wa'adin watanni uku ya kammala aikinsa ya kuma mika rahoto.

Sai dai kuma bisa ga dukkan alamu wannan dakatarwa ta bar baya da kura inda yan kwadago a hukumar suka ce ba zata sabu ba. shugaban ‘yan kwadagon Comrade shehu mohammed Gajo, ya shaidawa muryar Amurka cewa wannan dakatarwa ba a yita akan ka'ida ba, ba a yita da yawun wadanda suka nada babban sakataren ba,inda yace anyi dakatarwar a cikin son rai.

Ko a baya dai sai da ministan lafiya na kasa farfesa Isack Adewale ya dakatar da ministan, lokacin da shugaban kasa ke jinya a birnin Londan, amma bayan da shugan ya dawo ya bincika, bai sameshi da laifin kome ba sai ya soke dakatarwar kuma ya maida shi bakin aikinsa.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina

An dakatar da sakataren hukumar lafiya ta Najeriya-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG