Faduwar Darajar CEDI A Ghana Ya Haifar Da Tsadar Ruwan Sha 

Ghana cedi.

Mazauna birnin Accra a kasar Ghana sun fara kokawa bayan farashin ruwan leda ya yi tashin gwauron zabo inda aka koma sayar da jaka daya cidi 7 zuwa 8 kwatankwacin dala 1.

ACCRA, GHANA - Kungiyar masu sarrafa ruwan leda a Ghana tayi karin kudin ruwan biyo bayan karin kudin leda da faduwar darajar sidi, da kuma tsadar man fetir a kasar.

Mallam Attijani Hamza masanin tatalin arziki yayi sharhi a batun. Ya ce karin kudin ruwan leda wato pure water ya biyo bayan karin man fetur, da faduwa darajar cidi wanda hakan yayi sanadiyyar da kayayyakin sarrafa ruwa yayi tsada, ganin hakan suka kara na ruwan leda.

Tuni dai al’ummar kasar take kira ga gwamnati ta tallafa wa kungiyar masu saida ruwan leda, domin daidaita farashin.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hawa Abdul Karim:

Your browser doesn’t support HTML5

Faduwar Darajar CIDI A Ghana Ya Haifar Da Tsadar Ruwan Sha