Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Samu Shiga Gasar Cin Kofin Duniya Bayan Ta Lalasa Najeriya


Ghana ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za'a yi a Qatar biyo bayan nasara akan Super Eagles na tarayyar Najeriya a birnin Abuja.

KUMASI, GHANA -Bayan lashe gasar, wasu al’umman Ghana da dama sun ka fita tituna don nuna farin cikinsu.

Nasarar na zuwa ne bayan da ‘yan wasan Black Stars suka tashi da ci 1-1 da ‘yan wasan Super Eagles a karawar da suka yi a Abuja.

Sai dai minti 10 da fara wasan, dan wasan tsakiyar Ghana Black Stars Thomas Partey ya zura kwallo a ragar Najeriya . Daga baya Najeriya ta rama ta hannun William Ekong minti 12 tsakani da bugun fenarti.

Najeriya ta samu damar zura kwallo ta biyu ta hannun Victor Osimhen, amma alkalin wasan ya soke kwallon bayan da aka gano cewa Osimhen ya yi satar gida.

Wasu yan Najeriya da suka tattaru suna kallon wasan abirnin Kumasi suna ganin rashin kawo Ahmed Musah da Ighalo da wuri na daga cikin dalilan da ya sa Najeriya rashin nasara awasan.

Aranar Juma'a na makon jiya Super Eagles ta tashi babu ci da Black Stars a garin Kumasi a wasan farko.

Wannan shi ne karo na hudu da Ghana za ta halarci gasar cin kofin duniya, Ita kuwa Najeriya da tayi nasara, da zuwanta na bakwai kenan.

‘Yan Wasan Kwallon Kafa Na Kamaru
‘Yan Wasan Kwallon Kafa Na Kamaru

A halin da ake ciki kuma, Kamaru ta yi wa Aljeriya dukan ba zata da ci 2 da 1 a birnin Blida. Hakan ya kasance ne a karewar zagaye na biyu tsakanin wadannan ƙasashen.

Éric Maxime Choupo-Moting kaftin na yan Kamaru ne ya fara bude raga a mintuna 22 da fara wasa. Hakan ya daidaita kasashen biyu saboda Aljeriya ta doke Kamaru a zagayen farko da aka buga a Douala ci 1 da banza.

Sai dai da aka je zangon karin lokaci, Aljeriya ta zura kwallo daya a mintuna 118, dab da karshen wasa.

A mintin karshe Karl Toko Ekambi ya zura kwallon da ta baiwa Indomitable Lions tikitin zuwa Qatar.

Mogoya bayan Kamaru sun hana idanunsu bacci domin farin ciki.

XS
SM
MD
LG