Fara Hakar Mai A Arewacin Najeriya Zai Kawo Bunkasar Tattalin Arzikin Yankin Da Ma Kasar - Kwararru

Albarkatun mai 

Shirin hako danyen mai na farko  da gwamnatin Najeriya ta yi a yankin Kolmani da ke kan iyakar Jihar Bauchi da Gombe, wadanda ke yankin arewa maso gabashin kasar, zai kawo cigaba da karshen dogaro ga man ,kudu da arewa ke yi.

A yanzu haka dai jihohin biyu za su shiga jerin jihohi 9 da ke da arzikin man su zama jihohi 11, wadanda kundin tsarin kasa ya tanadi a ba kaso 13 cikin 100 na man da aka samu duk wata.

To ko ya ake ganin wannan cigaba da yankin ya samu, kuma hakan zai rage zaman doya da manja da ake yi tsakanin yankin arewa da kudancin kasar wadanda tuni suka dade a fannin hako man?

Albarkatun mai

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya na gannin wannan ba karamin cigaba yankin arewacin kasar ya samu ba, mussaman idan aka yi la'akari da dimbin albarkatun man da za a amfana da shi daga wadannan jihohin kamar yadda Muhammad Saleh Hassan kwararre a harkar man fetur da iskar gas a Najeriya ya bayyana.

Ku Duba Wannan Ma Ana Tuhumar Wasu Mutane 26 Da Ake Zargi Da Satar Danyen Mai

Toh sai dai a yayin da ake marhabin da wannan ci gaba, wani abun daukar hankali shi ne batun tsaro, la'akari da tsawon shekarun da aka shafe ana fama da shi a yankunan da suka dade a harkar, kamar yadda masana tsaro ke gargadi a kai.

Ana dai ganin soma aikin hakar mai a yankin arewacin Najeriya a halin yanzu, zai rage gorin da ta sha fuskanta a baya kan batun dogaro da man da ke fitowa daga kudancin Kasar.

Saurari cikakken rahoton daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

Fara Hakar Mai A Arewacin Najeriya Zai Kawo Karshen Dogaro Akan Yankin Kudancin Kasar.mp3