Firayim Ministan Italiya Ya Bada Sanarwar Yin Murabus

Firayim Ministan Italia Matteo Renzi

Akwai alamun dake nuna cewa kasar Italiya ta kama hanyar abkawa cikin wani sabon rikicin siyasar da za’ayi makkoni ana fama da shi, bayanda al’ummar kasar suka juya bayansu ga yunkurin da Firayim Ministan kasar yayi na kawo wasu sauye-sauye a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Wannan yunkurin na Firayim Ministan, Matteo Renzi, ya sashi dole ya bada sanarwar cewa yayi murabus.

A wajen wata ganawa da manema labarai da aka yi sauri aka shirya sa’oi biyu kacal bayanda aka rufe rumfunan jefa kujri’un bayyana ra’ayoyin na jama’a, Firayim Minista Renzi, 41, ya amsa cewa lalle ya sha kaye a wannan kuri’ar da aka jefa.

Yace a yau Litinin ne zai hannunta takardarsa ta yin murabus ga shugaban Italiya din, Sergio Mattarella.

Sakamakon da aka samu daga larduna 20 na kasar dai sun nuna cewa kashi 59.3 cikin 100 na masu bayyana ra’ayin sun ki goyon bayan shirin sauye-sauyen na Pr.ministan, yayinda ya sami goyon bayan kashi 40.7%.