Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin da Ya Kai Ayyukan Sarafa Kayansa Waje Zai Biya Zunzurutun Haraji - Trump


Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado
Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ja kunnen kampunna da masana’antun dake Amurka din da cewa daga yanzu duk dayansu da ya sake neman tashi ya bar Amurka zuwa komawa wata kasar wajen zai fuskanci zunzurutun harajin kashi 35% idan yace zai kawo hajarsa cikin Amurka ya saida ta.

A cikin wasu rubuce-rubucen da ya sako akan danmdalinsa na Twitter ne Trump yake bayyana kudurinsa na bunkasa harakokin kasuwanci idan ya kama aiki gadan-gadan, amma ya kara da kasedin cewa duk kampanin dake zaton zai kori ma’aikatansa ko ya koma wata kasar waje, wai zai dawo ya rinka sayarda hajar tasa a nan Amurka ba tareda wasu matakan horo a kansa ba, to yana tapka kuskure ne kawai.

Haka kuma Trump, wanda zai dare kan shugabancin Amurka ran 20 ga watan Janaikrun sabuwar shekara, yace dimbin harajin tsallako kan iyakokin Amurka da kaya da zai dorawa kayan da ake sarrafawa a wasu kasashe, ana son a shigo da su zuwa cikin Amurka, zai kashe jikin duk masu tunanin irin wannan nau’i na kasuwanci.

Daga shekarar 2000 zuwa yau dai Amurka tayi asaran aiyukka sun kai milyan 5 a sanadin soma anfani da injuna masu anfani da komputoci da kuma kudurin wasu kampunna na tashi suna komawa kasashen ketare.

XS
SM
MD
LG