'Yar Majalisa: Ba Za Mu Manta Da 'Yan Matan Chibok Ba

Taron Tuna 'Yan Matan Chibok

An gudanar da wani taro a Amurka, domin yin tuni kan sauran ‘yan matan makarantar Sakandare na garin Chibok da mayakan Boko Haram suka sace a jihar Borno da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya a shekarar 2014.

Taron, wanda ‘yar majalisar wakilan Amurka, Frederica Wilson, da fitacciyar ‘yar jarida Isha Sesay suka shirya, ya gudana ne a gini Majalisar Dokokin kasar a jiya Alhamis.

Isha Sasey Dauke Da Littafin Da Ta Rubuta A Taron Tuna 'Yan Matan Chibok

Yayin wannan taro, an ba da lambar yabo ga Sesay wacce ta rubuta littafi mai taken “Beneath the Tamarind Tree,” wanda ya ba da labarin 'yan matan, da yadda aka sace su, da kuma irin wahalar da suke sha a hannun 'yan Boko Haram.

Isha ta je har Najeriya inda ta ji ta bakin wasu daga cikin 'yan matan, da kuma iyayensu kafin ta rubuta wannan litafi, wanda a cewarta, ta yi hakan ne don kar a manta da 'yan matan, da labarinsu.

Patricia Bulus Da Isha Sasey A Taron Tuna 'Yan Matan Chibok

Wani babban al’amari da ya sosa wa mahalarta taron rai shi ne, lokacin da Patricia Bulus daya daga cikin matan da suka kubuta ta yi magana. Ta bayyana rayuwarta, da tsabar tashin hankalin da suka gani lokacin da aka dauke su.

Yayin jawabinta, ‘yar majalisa Wilson, ta yi bayani kan wata ziyarar da ta kai Najeriya, inda ta ce ta yi kuka da hawaye a lokacin da ta ji labarinsu. Kuma ba tare da ba ta lokaci ba, a lokacin ta ce akwai bukatar su tallafa.

A tsakanin ranakun 14-15 ga watan Afrilu, mayakan Boko Haram suka sace ‘yan matakan makarantar ta Chibok su 276.

Taron Tuna 'Yan Matan Chibok

An dai samu damar kubutar da wasu daga cikinsu, amma har yanzu akwai da dama da ke ci gaba da zama a hannun mayakan na Boko Haram.