Gasar Zakarun Turai: AC Milan Da Bayern Munich Sun Yi Nasara

Champions League - Wasan Farko Na Zagayen 'Yan 16 - AC Milan da Tottenham Hotspur

Kwallon farko da Brahim Diaz ya zura a raga tun watan Oktoban bara ta bai wa Milan nasara a kan Tottenham da ci 1-0, a wasan farko na zagayen ‘yan 16 na gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Diaz ya buga wasannin 12 ba tare da zura kwallo ba a gasar Serie A, amma ya zura kwallo a ragar Spurs da wuri da kai a ranar Talata.

Tottenham ta samu damarmaki na zura kwallo amma ta gaza farkewa a kan ‘yan wasan tsohon kocin Inter Millan Antonio Conte da ya koma zuwa San Siro.

Milan ta yi wasanni bakwai ba tare da nasara ba kafin ta ci Torino a ranar Juma’a da ta wuce, amma Diaz ya bata nasara biyu a jere da kuma hakan zai bata ‘yar dama da za ta fafata a wasa na biyu a filin wasa na Tottenham Hotspur a ranar 8 ga watan Maris.

Champions League - Zagayen Farko Na 'Yan 16 - AC Milan da Tottenham Hotspur

A daya wasan kuma, Kingsley Coman ya zura wata muhimmiyar kwallo a gasar Champions Leage a kan tsohuwar kungiyarsa ta Paris Saint-German, yayin da Bayern Munich ta ci 1-0 a wasan da ta buga a waje da suka fafata a zagayen ‘yan 16.

Coman haifaffen Paris ya zura kwallo daya tilo a lokacin da Bayern ta doke PSG a wasan karshe shekaru uku da suka gabata, kuma ya maimaita wannan dabara a filin wasa na Parc des Princes a ranar Talata.

Champions League - Zagayen 'Yan 16 - Paris St Germain da Bayern Munich

Bayern ta cancanci samun nasara a wasan farkon, kuma babbar kungiyar ta Bundesliga tana fatan ba za ta fuskanci kalubale ba na yin nasara da kwallo daya tilo a kan PSG, wacce ta yi wasa ba tare da Kylian Mbappe ba har zuwa minti na 57.

Mbappe, wanda ya dawo daga jinyar rauni, an saka shi jim kadan bayan kwallon da Coman ya ci, kuma ya kasa sauya wasan, ganin an hana kwallon da ya farke, amma kasancewarsa a wasan na biyu da za’a buga a Jamus yana iya yin tasiri.