Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Lallai Mbappe Ya Buga Wasan Bayern Munich Ba


Ligue 1 - Montpellier da Paris St Germain
Ligue 1 - Montpellier da Paris St Germain

Da alama Kylian Mbappe ba zai buga wasan da Paris Saint-Germain za ta yi da Bayern Munich a wasan zagayen farko na ‘yan 16 a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League saboda raunin da ya ji a kafarsa.

Dan wasan gaban mai shekaru 24 da haihuwa yaji rauni a farkon rabin lokaci a wasan da PSG ta doke Montpellier da ci 3-1 a ranar Laraba da ta gabata, kuma zai yi jinyar kusan makonnin uku.

Zakarun na Faransa sun fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis, inda suka bayyana kiyasin lokacin da Mbappe zai warke, wanda idan har gaskiya ne ba zai buga wasannin lig da za su kara da Touluse, Monaco da Lille ba, da wasan Coupe de France da Marseille, da kuma wasansu na farko a gasar Zakarun Turai a gida da Bayern, wanda za’a yi a ranar 14 ga watan Fabrairu.

“Bayan gwaje-gwaje, Kylian Mbappe ya samu rauni a cinyarsa ta hagu. An kiyasta lokacin da zai dawo zuwa makonnin uku,” in ji kungiyar PSG.

Ligue 1 - Montpellier da Paris St Germain
Ligue 1 - Montpellier da Paris St Germain

Mbappe, wanda ya zura kwallaye 25 a wasanni 26 da ya buga wa PSG a kakar wasa ta bana, ya yi wasan da ba zai manta ba a ranar Laraba, yayin da mai tsaron raga ya buge fenaratin da ya buga, ciki har da wadda ya sake bugawa ta yi sama, sannan ya fito da rauni a minti na 21 da fara wasa.

Kulab din ya kuma tabbatar da cewa za’a yi wa Sergio Ramos gwaje-gwaje, bayan da tsohon dan bayan Sipaniya shi ma aka cire shi a karawar da suka yi da Montpellier bayan da yaji rauni a kai.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG