Ghana Ta Sallami Mai Horar Da Black Stars

Milovan Rajevac

A watan Satumba aka dauki Rajevac a matsayin kocin ‘yan wasan na Black Stars a karo na biyu.

Ghana ta sallami mai horar da ‘yan wasanta na Black Stars bayan rashin taka rawar gani da ya kai ga saurin ficewar kasar a gasar cin kofin kasashen Afirka da ake yi a Kamaru.

Tun a ranar Laraba hukumomin kasar suka yanke hukuncin sallamar Milovan Rajevac a cewar AP.

Yanzu ya zama dole tawagar ‘yan wasan ta samu mai horar da ita gabanin karawarta da Najeriya a wasanni biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za su yi a watan Maris.

Ghana, wacce ta taba lashe kofin na AFCON sau hudu, ta yi sammakon ficewa daga gasar bayan da ta samu maki daya kacal a wasannin da ta buga da Morocco, Gabon da kuma Comoros.

Ku Duba Wannan Ma AFCON: Comoros Ta Kada Ghana Gida Bayan Ta Lallasa Ta Da Ci 3-2

Comoros, wacce wannan shi ne karonta na farkon na zuwa gasar, ta yi ajalin Ghana a gasar, abin da ya girgiza masu sha’awar kwallon kafa.

A watan Satumba aka dauki Rajevac a matsayin kocin ‘yan wasan na Black Stars a karo na biyu.

Kocin wanda dan asalin kasar Serbia ne, ya taba horar da Ghana a tsakanin 2008-2010, inda ya kai ta zagayen quarter-finals a gasar cin kofin duniya a 2010.