Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFCON: ‘Yan wasan Ghana Sun Kafa Sansani A Birnin Doha


'Yan wasa Ghana suna atisaye a birnin Doha (Facebook/Hukumar kwallon kafar Ghana)

Hukumar kwallon kafar kasar ta Ghana ta ce ya zuwa ranar Litinin ‘yan wasa na Black Stars sun fara hallara a sansanin da ke kasar ta Qatar.

‘Yan wasan Ghana Black Stars sun kafa sansaninsu a Doha, babban birnin Qatar gabanin fara gasar cin kofin nahiyar Afirka.

A ranar 9 ga watan Janairun 2022 za a bude gasar a kasar Kamaru da ke karbar bakuncin gasar

Kasashe 24 ne za su fafata don neman lashe kofin.

Hukumar kwallon kafar kasar ta Ghana ta ce ya zuwa ranar Litinin ‘yan wasa kasar sun fara hallara a sansanin.

“‘Yan wasan da suka shiga sansanin sun hada da Richard Atta, Lawrence Ati Zigi, Alexander Djiku, Mubarak Wakaso, David Abagna, Daniel Kofi Kyereh.

Sauran sun hada da, “Gideon Mensah, Abdul Fatawu Issahaku, da Maxwell Abbey Quaye.” In ji hukumar kwallon kafa ta Ghana.

Ghana na rukunin C, da ke dauke da Morocco, Gabon da kuma Comoros.

A ranar bakwai ga watan Janairu ‘yan wasan na Black Stars za su isa kasar ta Kamaru.

Za ta fara wasanta na farko da Morocco a gasar wacce za a kammala a ranar 6 ga watan Fabrairu.

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG