Gobara Ta Lakume Shaguna 100, Miliyoyin Kudade a Abia

Yadda gobara ta lakume kasuwar dabbobi ta Lonkpanta a jihar Abia

Rahotanni daga jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya na cewa, wata gobara da ta shi a kasuwar sayar da dabbobi da fatu, ta lakume shaguna sama da 100 da kudaden da har yanzu ba a tabbatar da yawansu ba.

Hukumomin kasuwar sun ce gobarar ta tashi ne da safiyar jiya Juma’a.

“Alhamdulillah, ba a yi asarar rai ba, amma dai an yi asarar dukiya wacce ba za ma a iya kimanta wa ko ta kai miliyan 100 ba,” a cewar Sakataren kasuwar wacce ke garin Lonkpanta, wato Malam Awwal Hamman.

Sai Hamman wanda ya danganta lamarin da jarrabawa daga Allah ya ce, akwai alamun wutar lantarki ce ta janyo gobarar ta kama katakwaye,

Kiyasin da aka yi, ya nuna cewa, shaguna fiye da 100 ne suka kone.

"Ita wannan gobarar masifa ce Allah ya kawo, ba za mu iya cewa ga musabbabin wannan wuta ba.” Ya ce.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Abia da ta tarayya da su kai masu dauki.

“Saboda bayin Allah da wannan abu ya same su abin tausayi ne, wani ba shi da inda zai je, wani ban da suturar da ke jikinsa ba shi da wata.”

Saurari cikakkiyar hirar Alphonsu Okoroigwe da Malam Awwal Hamma:

Your browser doesn’t support HTML5

Gobara Ta Lakume Shaguna 100, Miliyoyin Kudade a Abia - 1'05"