GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Yuni 28, 2018: Bibiya Kan Tsarin Ciyar Da Yara A Makarantun Gwamnatin Najeriya Kashi Na Daya

Grace Alheri Abdu

yau shirin Domin Iyali ya gayyaci masu ruwa da tsaki domin neman hanyar inganta shirin ciyar da yara da abinci a makarantun gwamnatin Najeriya, inda yanzu haka ake gudanar da shirin a matsayin gwaji a jihohi 24 na kasar da kuma birnin Taraya Abuja.

Masu ruwa da tsaki da shirin ya hallara domin bibiya kan wannan batun da sun hada da

sun kuma tattauna kan yadda shirin yake tafiya, da kalubalai da ake fuskanta, da kuma matakan da za a bi na gyara.Mun kuma nazarci abinda aka yi, da abinda ba a yi ba, da kuma nasarorin da shirin ya cimma da al'amuran da suka jibinci aiwatar da wannan shirin.

Domin nazari a kan wannan batu, shirin ya gayyaci Mallam Sani Rabi'u, shugaban makarantar firamare da Janbulo a birnin Kano, da Kwamred Tahir Mahmud Saleh, babban jami'i a wata kungiya da ake kira Bridge Nigeria Initiative masu rajin bunkasa harkokin ilimi musamman a yankunan karkara, a wadansu jihohin arewacin Najeriya, sai kuma Mallam Abdullahi Ja'afar wanda yake daga cikin rukunin wadanda aka dauka a tsarin wucin gadi don bibiyar yadda al'amuran suke tafiya a wadansu daga cikin makarantun jihar Kano

Ga jagoran tattaunawar Mahmud Ibrahim Kwari da kashi na daya na wannan tattaunawar.

Your browser doesn’t support HTML5

Bibiya Kan Ciyar Da yara da abinci a makarantu-10:25"