Gubar dalma ta kashe kananan Yara 400 a jihar Zamfara

Wadansu kananan yara a kofar gida

Cibiyar Human Right Watch tace kananan yara dari hudu sun mutu ta dalilin gubar dalma.

Cibiyar Human Right Watch tace kananan yara dari hudu sun mutu ta dalilin gubar dalma.

Bisa ga rahoton cibiyar Human Right Watch, kauyukan da abin yafi shafa sun hada da Abare, da Dareta da Duza da Sunke da kuma Tungar Daji. Sauran kuma sune Tungar Guru da Yargalma, yayinda ake kyautata zaton rasa rayukan kimanin kashi arba’in bisa dari na yaran da suka nuna alamun harbuwa da gubar dalmar.

Wakiliyar Human Right Watch a Najeriya Jane Cohen tace, kananan yara da dama sun dakuna gubar tun shekaru biyu da suka shige abinda ya sa lamarin ya zama annoba a tsakanin al’ummar.

Lokacin da take nuna hoton bidiyon matsalar, Cohen tace duk da yake an yi kiyasin cewa, kananan yara dari hudu sun rasa rayukansu, har yanzu ba a fara aikin tsabtace muhallun kauyaka da dama da abin ya shafa ba.

Human Rights Watch tace ana aikin hakar zinari a ko’ina cikin jihar Zamfara kuma yawan dalma mai guba dake karkashin kasa da kuma hanyoyin hakar kuzan ya jefa kananan yara cikin hadarin annoban dalma mai guba.

Binciken da cibiyar Humar Rights ta gudanar ya kuma nuna cewa, yara suna taba dalmar mai guba lokacin da suke rairaye dusar zinarin a ramukan da ake haka ko kuma lokacin da ake rairaye shi a gida, ko daga jikin iyayensu da suka dawo daga hakar zinarin.

Aika Sharhinka