Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cibiyoyi sun hada hannu domin samar da maganin zazzabin cizon sauro mai arha a Najeriya


Wadansu kananan yara dake jinyar zazzabin cizon sauro a asibiti
Wadansu kananan yara dake jinyar zazzabin cizon sauro a asibiti

Najeriya tana kan hanyar samun maganin rigakafin zazzabin cizon sauro mai arha.

Najeriya tana kan hanyar samun maganin rigakafin zazzabin cizon sauro mai arha. Wannan ya biyo bayan hada hannu da wata cibiyar hadin guiwa dake aiki domin inganta ayyukan kiwon lafiya ta kasar Turai da ake kira PATHS2( Partnership for Transforming Health Systems) da hukumar bunkasa kasashen ketare (DFID) ta dauki nauyi.

Za a gudanar da shirin na inganta hanyoyin rigakafin zazzabin cizon sauro masu saukin kudin ne, tare da hadin guiwar shirin jinya da ake kira Clinton Health Access Initiative (CHAI) na tsohon shugaban kasar Amurka, da ma’aikatar lafiya ta Tarayya, da kamfanonin harhada magunguna dake kasar karkashin shirin samar da cibiyoyin maganin zazzabin cizon sauro mai arha (AMFm).

Za a gudanar da shirin ne da nufin samar a magungunan da gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da su na jinyar nau’in cutar malariya da bashi da wuyar jinya.

A karkashin shirin, za a samar da irin wadannan magungunan a dakunan shan magani musamman ga al’ummomin yankunan karkara na jihohin Lagos, da Kaduna, da Jigawa da Enugu da kuma Kano, jihohin da shirin PATHS2 zai dauki nauyi. An kuma yi kiyasin kashe Naira sittin kan kowanne mai jinya a maimakon naira dari takwas zuwa dubu biyu da shirin da ake aiwatarwa a halin yanzu yake kashewa kan magungunan jinya.

Wannan maganin zai kasance maganin jinyar zazzabin cizon sauro mafi arha a duk fadin Najeriya. Kawo yanzu mazauna yankunan karkara basu iya sayen maganin zazzabin cizon sauro sabili da tsada, amma tare da taimakon PATHS2 karkashin wannan shirin, za a samar da magunguna da rahusa kuma masu inganci kasancewa fitattun kamfanonin da hukumar lafiya ta duniya ke hulda da su ne zasu sarrafa magungunan.

An kaddamar da wannan shirine ne a Najeriya cikin shekara ta dubu biyu da biyar domin jinyar cutar malariya da bata jin magani, sabili da yawan amfani da maganin kuni da SP, magungunan zazzabin cizon sauro da aka dade ana amfani da su.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG